Matasa sun yi zanga-zanga akan rashin wutar lantarki a jihar Niger

Matasa sun yi zanga-zanga akan rashin wutar lantarki a jihar Niger

- Matasa a jihar Niger sun gudanar da zanga-zanga

- An yi zanga-zangan ne sakamakon rashin samun wutar lantarki yadda ya kamata a jihar

- A baya sun ba kamfanin wutar lantarki wa'adin wasu makonni domin ta inganta ayyukanta ko ta bar jihar

Matasa sunyi zanga-zanga a ranar Alhamis 18 ga watan Janairu akan rashin wutan lantarki daga kamfanin Abuja dake rabe-raben wutar lantarki.

Matasa sun fito kwansu da kwarkwatansu a fadin jihar Niger domin nuna adawa ga rashin samun isashen wutar lantarki.

A watan Oktoba na shekara da ya gabata ne, matasa suka ba kamfanin wutar lantarki da kamfanin sadarwa wa’adin tsawon sati hudu a jihar da su inganta wutar lantarki ko kuma su bar jihar.

Matasa sun yi zanga-zanga akan rashin wutar lantarki a jihar Niger

Matasa sun yi zanga-zanga akan rashin wutar lantarki a jihar Niger

Amman gwamnatin jihar, hade da majalisan dokokin jihar, sun tattauna akan al’amarin.

KU KARANTA KUMA: Martanin Fati Mohammed ga wasikar da wani Malam Datti Assalafiy ya aika mata

Yayinda matasan ke magana da wakilan gidan talabijin na Channels, matasan duk da haka, sun fahimci cewa basu gamsu da sakamakon shawarar da aka yanke ba, dalilin hakan ne yasa suka yanke shawarar aiwatar da zanga-zangan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel