Paul Unongo ya sauka daga matsayin shugaban kungiyar Dattawan Arewa (NEF)

Paul Unongo ya sauka daga matsayin shugaban kungiyar Dattawan Arewa (NEF)

- Shugaban kungiyar Dattawan Arewa Paul Unongo sauka daga kan mukamin sa a ranar Talata

- Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta ce zata nada sabon shugaban a cikin 'yan kwanakin kadan

Dr Paul Unongo ya sauka daga kan mukamin sa na matsayin shugaban kungiyar dattawan Arewa ( NEF) a ranar Talata bayan kungiyar ta gudanar da taron gaggawa a Abuja.

Legit.ng ta samu rahoton cewa, Dr Paul Unongo ya kira taron da kansa, inda ya sanar da mambobin kungiyar NEF ya sauka daga kan mukamin sa.

Wani majiya mai karfi ya fadawa manema labaru cewa kungiyar zata nada sabon shugaban da zai maye gurbin Dr Paul Unongo a cikin ‘yan kwanaki kadan.

Paul Unongo ya sauka daga matsayin shugaban kungiyar Dattawan Arewa (NEF)

Paul Unongo ya sauka daga matsayin shugaban kungiyar Dattawan Arewa (NEF)

Dr Paul Unongo ya fadawa manema labaru cewa ya sauka daga kan mukamin sa ne, saboda lokacin da zai ba kungiyar NEF damar fitar da sabon shugaba da zai kawo wa kungiyar cigaba.

KU KARANTA : Shittu ya zargi Ajimobi da nuna bangaranci da raba kawunan yan APC a jihar Oyo a wasikar da ya rubutawa Buhari

Ya kungiyar ta amince da hukuncin da ya yanke na sauka daga mukamin sa dan ba sabon shugaba dama, kuma sun bashi damar zaban musu sabon shugaba kungiyar.

Amma ya ce musu, su zaba duk wanda suke so ya zama shugaban su, kuma zan basu cikakkyar hadin kai,” inji Dr Paul Unongo.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel