Zai yi matukar wahala Buhari ya sake nasarar zabe a 2019 - Sheikh Gumi

Zai yi matukar wahala Buhari ya sake nasarar zabe a 2019 - Sheikh Gumi

Rahotanni sun kawo cewa shahararren malamin nan na addinin Musulunci dake zaune a jihar Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya yi hasashe game da zaben 2019 akan shugaba Muhammadu Buhari.

A cewar malamin zai yi wahala matuka ace shugaban kasa Buhari ya sake nasara a zaben 2019 saboda jama’an Najeriya zasu juya masa baya.

Haka zalika malamin ya bayyana cewa nasarar zaben shugaba Buhari ya danganta da wanda zasu fafata da shi.

Zai yi matukar wahala Buhari ya sake nasarar zabe a 2019 - Sheikh Gumi

Zai yi matukar wahala Buhari ya sake nasarar zabe a 2019 - Sheikh Gumi

Shafin rariya ta rahoto inda Sheik Gumi ya kara da cewa Buhari ya kasa cika alkawurran da ya daukarwa 'yan Najeriya sannan kuma ya saki ragamar mulkin a hannun wasu dake tafiyar da gwamnati tamkar ya zama Shugaban je-ka- na-yi- ka.

KU KARANTA KUMA: Shugaban Kasa Buhari zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron AU

Daga karshe ya kara da cewa Buhari ya kulla yarjejeniyar siyasa da mutanen Kudancin kasar nan wadanda suka taimaka masa ya ci zabe amma kuma an wayi gari suna ganin wasu sun yi babakere a gwamnatin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel