Daɗin abin za’a hadu a kiyama: Alkali ya yanke ma masu fyaɗe hukuncin bulala 6 a Katsina

Daɗin abin za’a hadu a kiyama: Alkali ya yanke ma masu fyaɗe hukuncin bulala 6 a Katsina

Wata kotun Majistri dake jihar Katsina ta yanke ma wasu matasa su hudu da aka kama da laifin aikata fyade hukuncin bulala shida shida, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito matasan da suka hada da Ahmed Lawal, Abdulmalik Mustapha, Adamu Khalid da Abubakar Lawal sun samu wannan sassauci ne bayan da suka amsa lafinsu a gaban Kotun.

KU KARANTA: Daliban jihar Kaduna sun yi madalla da matakin sallamar Malamai a jihar

Da take yanke hukuncin, Alkalin Kotun, Fadila Dikko ta bayyana cewar kotun ta yanke wannan hukunci ne biyo bayan neman afuwa da matasan suka yi a gaban kotu, haka zalika basu ba shari’a wahala ba, kuma wannan shi ne karo na farko da suka taba aikata mummunan laifin.

Daɗin abin za’a hadu a kiyama: Alkali ya yanke ma masu fyaɗe hukuncin bulala 6 a Katsina

Fyade

Su dai wadannan matasa mazauna unguwar Rafukka, sun sace wasu yan mata guda biyu ne dga unguwar Abbatuwa, suka kaisu wani kango, inda kowannensu ya zakke ma kowacce daga cikin yan kananan yaran.

Sai dai baya ga hukuncin bulalar, Kotun ta yanke musu hukuncin zaman gidan kaso na wata biyar bisa tuhumar sace yaran da kuma na yi musu fyade, amma ta basu zabin biyan jimillan kudi naira 7,000.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel