Matasan Kungiyar Ohanaeze Ndigbo sun umurci makiyaya su fice daga yankin Kudu

Matasan Kungiyar Ohanaeze Ndigbo sun umurci makiyaya su fice daga yankin Kudu

- Matasan Kungiyar Ohanaeze Ndigbo sun bukaci dukkan Makiyaya da ke yankin Kudu maso Gabashin kasar nan su gagauta barin yankin

- Matasan kuma sun bukaci Gwamnatin Tarayyah ta kafa filayen kiwo aladu a yankin Arewa kamar yadda ta ke yunkurin kafa filayen kiwo shanu a kudu

- Matasan sun kuma bukacin Gwamnatin Tarayyah ta bayana Kungiyar Miyetti Allah a matsayin kungiyar ta'addanci

A ranar Laraba ne reshen matasa na sananiyar kungiyar kabilar ibo 'Ohanaeze Ndigbo' ta umurci dukkan makiyaya da ke yankin Kudu maso Gabashin kasar nan su tattara yanasu-yanasu su bar yankin.

Matasan kuma sun bukaci Gwamnatin Tarayyah ta haramta ayyukan Kungiyar makiyaya na Miyetti Allah na kasa, su kuma ambata Kungiyar a matsayin kungiyar yan ta'adda. Kazalika, Kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Tarayyah ta kafa filayen kiwon Aladu a yankin Arewa domin al'ummar Ibo da ke zama a Arewan.

Matasan Kungiyar Ohanaeze sun kori makiyaya daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya

Matasan Kungiyar Ohanaeze sun kori makiyaya daga yankin Kudu maso Gabashin Najeriya

KU KARANTA: Sojin Najeriya sun kama buhunan ganyen wiwi 63

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Okechukwu Isiguzoro, Sakatare Janar, Okwu Nnabuike da kuma Sakataren yadda labaran kungiyar, Obinna Adibe. Sanarwan ta ce Kungiyar ta cin ma wannan matsayan ne bayan wani taro da sukayi domin tattaunawa kan hare-haren da makiyaya ke kaiwa a wasu sassan Najeriya.

Sanarwan ta cigaba da cewa Kungiyar ta haramtawa dukkan Makiyaya da ke kananan hukumomi 95 na yankin kiwo kuma ta gargadi duk wani Makiyayi da yaki barin yankin na su ya kuka da kansa.

Kungiyar kuma ta yabawa wa Gwamnonin Jihohin Abia da Anambra bisa yadda suka ki amincewa da dokar kafa filayen kiwo na makiyaya a jihohin nasu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel