Sojin Najeriya sun kama buhunan ganyen wiwi 63

Sojin Najeriya sun kama buhunan ganyen wiwi 63

- Jami'an Rundunar Sojin Najeriya sunyi nasarar cafke buhunan ganyen wiwi 63 daga hannun wasu miyagu

- Rundunar ta kai sameme wata jeji ne a garin Owo bayan samun bayanan sirri daga wata majiya

- Bayan musayanan wuta, jami'an rundunar sunyi galaba kan bata garin

Jami'an hukumar Sojin Najeriya na 32 Artillery Briged da ke Akure sunyi nasarar kama buhunan ganyen wiwi 63 a wani gari mai suna Owo da ke karamar hukumar Owo na jihar Ondo. Mataimakin Direktan hulda da jama'a na Briged din, Manjo Ojo Adelegan ne ya sanar da hakan a ranar Laraba.

Sojin Najeriya sun kama buhunan ganyen wiwi 63

Sojin Najeriya sun kama buhunan ganyen wiwi 63

A cewarsa, Jami'an rundunar sun kai samame ne cikin wata daji da ke Owo bayan sun sami bayanan sirri daga wata majiya. Adelegan yace bata gari ne sukayi katutu a dajin.

KU KARANTA: Ba mu da filayen kiwon shanu, in ji Gwamnatin Jihar Taraba

Ya cigaba da cewa jami'an rundunar sunyi musayar wuta da bata garin amma daga bayan sojin sukayi galaba a kansu, bayan buhunan ganyen wiwi din guda 63, rundunar sun kwace harsashin bindiga guda 32.

Adelagan ya yi kira ga al'umman jihar su cigaba da taimakawa jami'antsaro da bayanan sirri da zai taimaka wajen magance masu aikata miyagun ayyuka. Ya kuma yi gargadi ga miyagu su fice daga jihar domin ba zasu sami gindin zama ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel