Zaben 2019: Kungiyar Ijaw sun kaddamar da goyon baya ga Atiku

Zaben 2019: Kungiyar Ijaw sun kaddamar da goyon baya ga Atiku

- Kungiyar siyasar kabilar Ijaw ta ce zata goyi bayan kudurin Atiku na tsayawa takarar kujeran shugabancin kasa

- Kungiyar ta ce tsohon mataimakin shugaban kasar zai kawo nasara ga jam’iyyar PDP

- Kungiyar ta bayyana Atiku a matsayin mutum mai iya daidaita kasar

Kungiyar siyasar kabilar Ijaw ta bayyana goyon bayanta ga tsohon mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar inda take cewa shugabancinsa zai zamo abun alkhairi ga kasar.

Atiku ya sauya sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP sannan ko da yake bai bayyana burinsa ga jama’a ba, akwai jita-jitan cewa zai tsaya takarar kujerar shugaban kasa.

Zaben 2019: Kungiyar Ijaw sun kaddamar da goyon baya ga Atiku

Zaben 2019: Kungiyar Ijaw sun kaddamar da goyon baya ga Atiku

Jaridar Vanguard ta rahoto jawabai daga bakunan shugaba da sakataren kungiyar, Oliver Isaac da Mista Ebikeme Banre, kungiyar ta ce amincewar Atiku a batun sake fasalin kasar zai kawo zaman lafiya ga kasar.

KU KARANTA KUMA: Shugaban Kasa Buhari zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron AU

“Shawarar komawa jam’iyyar PDP da ka dauka ya zo a lokacin da ya kamata sannan burinka na takarar kujerar shugaban kasa a 2019 abune da ya cancanci yabo kuma cigaba ne a tarihin Najeriya ga baki daya kamar yanda baka bi son zuciya ba.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel