Daliban jihar Kaduna sun yi madalla da matakin sallamar Malamai a jihar

Daliban jihar Kaduna sun yi madalla da matakin sallamar Malamai a jihar

Kungiyar daliban kwalejojin Ilimi na kasa, NAPS, ta bayyana goyon bayanta ga matakin sallamar Malamai sama da 20,000 da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai yayi don sauya fasalin ilimin jihar.

Daliban sun tabbatar da cewa sallaman Malaman da basu cancanta ba wani hanya ne na bunkasa samar da ingantaccen ilimi a matakin firamari, kamar yadda shugaban kungiyar, Mohammed Eneji ya bayyana ma jaridar Daily Trust.

KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi ya tofa albarkacin bakinsa kan rikicin makiyaya da manoma

Eneji ya nuna damuwarsa da tabarbarewa ilimi a kasar nan, inda yace matakin da gwamnan ya dauka yayi daidai duba da matsalar dake cike da harkar Ilimin Firamari, wanda shine ginshikin ilimin da zai sanya mutum ya amfani al’ummarsa a gaba.

Daga bisani majiyar Legit.ng ta ruwaito daliban sun yi kira ga Gwamna El-rufai daya gaggauta shirin dauka sabbin Malamai, kamar yadda ya fara, sa’annan sun yi kira ga sauran gwamnoni su yi koyi da El-Rufai.

“Ya zama wajibi mu dauki ilimin Firamari da muhimmanci, amma abin takaici shine ilimi na cigaba da lalacewa a Najeriya, don haka muke ganin matakin da gwamnan ya dauka yayi dace da hanyar sake farfado da ilmi a Najeriya gaba daya.” Inji shugaban.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel