Gwamnonin APC sun gujewa taron shugabannin jam'iyya

Gwamnonin APC sun gujewa taron shugabannin jam'iyya

A ranar Larabar da ta gabata ne, gwamnonin jam'iyyar APC suka watsa ƙasa a idanun shugabannin jam'iyyar wajen rashin halartar taron da aka shirya domin tattauna muhimman batutuwa na kasa.

Legit.ng ta fahimci cewa, an shirya taron ne domin tattauna alaƙoƙin dake tsakanin wasu gwamnonin APC game da al'amura na tsaro wadanda ke haifar da abin kunya ga jam'iyyar da gwamnatin tarayya baki daya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwe da Simon Lalong na jihar Filato shun shiga takun saƙa a kafofin watsa labarai dangane da sanya dokar hana kiwo a jihar ta Benuwe.

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan doka ta janyo ruguntsumi a tsakanin makiyaya da manoma dake ta haifar da salwantar rayuka da asarar dukiya.

Gwamnonin APC sun guje wa taron shugabannin jam'iyya

Gwamnonin APC sun guje wa taron shugabannin jam'iyya

Gwamnan Jihar Benuwe ya kuma shiga takun saƙa da takwaransa na jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura.

KARANTA KUMA: Hukumar fasaƙauri ta datse wata mota dauke da igiyar leko

Wata majiyar rahoto ta bayyana cewa, dalilin kiran wannan taro shine warware dukkan sa'insar dake tattare da dokar hana kiwo.

Ta ƙara da cewa, shugaban jam'iyyar, Cif John Odigie-Oyegun ya nufaci hada kawunan gwamnoni wuri guda domin sulhunta bambamce-bambamcen ra'ayoyinsu.

An sa ran cewa wannan taro zai ƙunshi shugabannin jam'iyyar, gwamnoni 24 da kuma jiga-jigan jam'iyyar dake majalisu na tarayya, inda mafi akasarin gwamnonin suka dirra a Abuja domin halartar taron wanda daga bisani aka dage zaman don gudun kar zaman ya sake janyo rabuwar kawuna a jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel