Shugaban Kasa Buhari zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron AU

Shugaban Kasa Buhari zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron AU

- Shugaba Buhari zai halarci wani taron Kungiyar AU a mako mai zuwa

- Shugaban Kasar ne babban mai jawabi game da yaki da rashin gaskiya

- Matan Shugabannin Kasashen Afrika za su yi wani taro na su a zaman

Shugaban Kasa Buhari zai jagoranci tawagar Najeriya zuwa taron AU

Buhari zai yi jawabi a wani taro na Kungiyar AU

Mun samu labarin cewa a makon gobe ne Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari zai jagoranci tawagar kasar zuwa wani muhimmin taro na Kungiyoyin Afrika watau AU a Kasar Habasha.

A mako mai zuwa Shugaba Buhari zai halarci taron Kungiyar AU ta Afrika na karo na 30 a babban birni Addis-Ababa. Mai magana da yawun bakin Ministan harkokin waje na Kasar Dr Tiwatope Elias-Fatile ta bayyana mana wannan.

KU KARANTA: Hadimin Shugaban kasa ya ba Makiyaya shawara

Shugaban Kasar zai yi jawabi a game da yaki da rashin gaskiya da Gwamnatin sa ta ke yi. Kungiyar kasashen Nahiyar sun nada Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin Jakadan yaki da rashin gaskiya a Afrika tun a kwanakin baya.

Bayan jawabi kan yadda aka samun nasara wajen yaki da barna a Kasar, Matan Shugabannin Kasashen na Afrika za su gana game da yadda za a kawo karshen cutar Kanjamau a Nahiyar ta Afrika da wasu batutuwa a zaman.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel