Gwamnatin Buhari ta saki Biliyan 30 da ma'aikata ke bi bashi tun lokacin Jonathan

Gwamnatin Buhari ta saki Biliyan 30 da ma'aikata ke bi bashi tun lokacin Jonathan

- Gwamnatin Shugaba Buhari ta biya ma'aikatan ta wasu makudan kudi

- Abin da aka ba Ma'ikatan Tarayya na kasar ya haura Naira Biliyan 22

- Za a kara sakin wasu kudin domin biyan bashi da ke kan Gwamnatin

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta biya ma'aikatan ta wasu makudan kudi da su ka dade su na sa rai za a biya su bayan sun samu karin matsayi a wajen aiki a Kasar kamar yadda mu ka samu labari.

Gwamnatin Buhari ta saki Biliyan 30 da ma'aikata ke bi bashi tun lokacin Jonathan

Buhari ya biya Ma'aikatan Gwamnati kudin su da ya dade

Daily Trust ta rahoto cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta ware sama da Naira Biliyan 30 domin biyan Ma'aikatan Gwamnatin Tarayyan Kasar wasu kudin da su ke bi tun daga 2011 har zuwa bara bayan an kara masu matsayi a ofis.

KU KARANTA: Ministan Buhari ya tsallake rijiya da baya -da baya

Babban Akanta na kasar nan Ahmed Idris ya tabbatar da wannan kwanan nan bayan da ya gana da Shugaban wani kwamiti da ke duba irin wadannan batutuwa. Akantan yace yanzu haka an ba Ma'aikatan kasar sama da Biliyan 22.

Yanzu haka ana sa ran sakin ragowar kudin da zarar an kammala aikin da ake yi na tabbatar da wadanda su ka cancanta a biya kudin. Akwai wasu Naira Biliyan 8 da 'yan kai yanzu da za a biya ragowar Maikatan da ba su samu rabon su ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel