Wata kotu ta gurfanar da mutane biyu da laifin zambar N15m a birnin tarayya

Wata kotu ta gurfanar da mutane biyu da laifin zambar N15m a birnin tarayya

Wata babbar kotun tarayya a Abuja, ta gurfanar da wasu maza biyu da ake zarginsu da zambar N15m a kamfanin da suke yiwa aiki.

Masu laifin, Mohammed Aliyu ɗan shekara 42 da kuma Isiaka Abubakar ɗan shekara 33, waɗanda duk ma'aikatan kamfanin Manipat Holdingne ne, sun gurfana a gaban kotu da laifin rashin gaskiya tare da wawuson dukiyar kamfanin.

Kotu ta gurfanar da mutane biyu a Abuja

Kotu ta gurfanar da mutane biyu a Abuja

Lauya mai shigar da ƙara, Barrister Patrick Omah, ya shaidawa kotun cewa waɗannan mutane biyu sun aikata laifin ne tun a watan Fabrairu da kuma Satumba na shekarar da ta gabata a yayin da suke aiki a karkashin kamfanin Manipat, inda suka yi sama da faɗi da zunzurutun kudi har N15m mallakar kamfanin.

KARANTA KUMA: Badaƙalar N92m: Hukumar EFCC ta cafke ɗan tsohon gwamnan jihar Nasarawa

Patrick yake cewa, sun aikata laifin ne ta hanyar ƙirƙirar takardun boge da sunan kamfanin.

A yayin da kotu ta karantawa waɗannan mutane biyu laifin da ake tuhumarsu da shi, sun bayyana rashin amincewar akan hakan.

Sai dai alƙalin kotun, Adebukola Banjoko, ya ɗaga sauraron ƙarar zuwa ranar 12 ga watan Fabrairu, inda ya umarci a ci gaba da tsare su a gidan kaso.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel