Hukumar fasaƙauri ta datse wata mota dauke da igiyar leko

Hukumar fasaƙauri ta datse wata mota dauke da igiyar leko

A halin yanzu, hukumar fasaƙauri reshen jihar Kaduna da Katsina tana ci gaba da tsananta bincike kan mutane shida da suka aikata laifukan sumoga a yayin da ta cafke wata motar tirela maƙire da gwanjon jakunkuna da kuɗin harajinsu kaɗai ya tasar ma naira miliyan takwas.

Shugaban hukumar reshen jihohi biyun, kwanturola Olusemire Kayode, shine ya bayyana hakan da cewar, an cafke waɗannan kayayyaki ne a lokutan bikin kirsimeti bayan tsawon makonni uku da suka dauka na gudanar da binciken diddigi.

Ma'aikatan hukumar fasaƙauri a yayin atisaye

Ma'aikatan hukumar fasaƙauri a yayin atisaye

A cewar sa, sauran kayayyakin da hukumar ta datse sun tasar ma N17.6 da suka hadar har da maganin sauro na igiyar leko.

KARANTA KUMA: Wani direban mota ya gurfana a gaban kuliya da laifin ɗauke matar maƙwabcinsa

Kayode ya bayyana cewa, babbar nasararsu itace irin jajircewa tare da sadaukar da kai na ma'aikatansu wajen fadi tashin hana shigo da kayayyakin da suka sabawa doka.

Ya kara da cewa, babu shakka sun bankado wasu sabbin hanyoyin da 'yan sumoga ke shigo da kayayyaki kasar nan, kuma suna daf da rufe wannan hanyoyi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel