Shugaban Innoson Motors ya yi watsi da goron gayyata na halartar zaman kotu

Shugaban Innoson Motors ya yi watsi da goron gayyata na halartar zaman kotu

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Innocent Chukwuma, shugaban kamfanin Innoson Motors bai halarci zaman kotun da aka gudanar a ranar Larabar da ta gabata ba.

Legit.ng ta fahimci cewa, babbar kotun birnin Ikeja dake jihar Legas, ta ci gaba da sauraron karar dake tsakanin shugaban kamfani da hukumar EFCC ke zarginsa da aikata laifuka sata da kuma zambar kudi.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya wato NAN ya ruwaito cewa, ana zargin Cif Innoson da kuma kamfaninsa Innoson Motors, sai dai wanda ake zargin bai halarci zaman kotu da aka shirya gudanarwa a yau laraba.

Cif Innoson Chukwuma

Cif Innoson Chukwuma

Jaridar ta kuma ruwaito cewa, za a gurfanar da wadanda ake tuhuma a kan laifin cin hanci da rashawa tare mallakar haramtacciyar dukiya ta hanyar zamba da ya aikata a tsakanin shekarar 2009 zuwa 2011 a jihar Legas.

KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya za ta saki fursunoni 368 a jihar Kano

Wannan laifuka sun sabawa sashe na 309,388, 465 da kuma 467 na dokokin jihar Legas kamar yadda hukumar EFCC ta bayyanar.

Mai shari'a Dada ya daga sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Fabrairu domin ci gaba da gudanar da takkadamar bincike.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel