Kannywood ta horas da matasa 450 harkar shirya fim

Kannywood ta horas da matasa 450 harkar shirya fim

- Ma'aikar Shirya Fina-finan Hausa (Kannywood) ta horas da matasa 450 shirin fim a fannoni mabanbanta

- Ta yi wannan horo ne don koyar da matasan harkar shirin fim ta zamani

- Ta kuma jawo hankulan su game da mutumcin hausawa da muhimmancin al'adun su

Hukumar Tace Finafinai na Jihar Kano, tare da hadin gwiwar Ma'aikatar Bincike da Koyar da Harkar fim na Pilato ta horas da matasa 450 harkar shirya fim din Hausa a fannoni daban daban.

Daraktan Gudanar na Hukumar Tace Finafinan, Muhammad Isma’ila Na’abba Afakallah, shi ne ya bayyana hakan ga manema labarai. Ya shaida masu cewan an bayar da wannan horo ne don matasan su samu ilimin shirya fim na zamani da kuma jaddada masu muhimmancin al'adun Hausa.

Kannywood ta horas da matasa 450 harkar shirya fim

Kannywood ta horas da matasa 450 harkar shirya fim

DUBA WANNAN: Babban magana! Wasu 'yan Najeriya za su shiga yajin aikin kin sayen nama

Don haka ne Afakallah ya yi kira ga 'yan fim da su zamanto masu daraja al'adun na Hausa, su kuma kiyaye duk wani abu da zai kawo batanci ga al'adun na Hausa ko kuma hausawa.

Ya kuma yi kira gare su da su tuna su musulmai ne kuma yaren da su ke fim din da shi yare ne na mutane masu mutumci wadanda kuma su ka dauki al'adun su da muhimmanci. Don haka dole me a yi taka tsantsan a kiyaye ma su mutumcin su.

Afakallah ya kuma yabawa Gwamnan Jihar ta Kano, Abdullahi Ganduje, game da habaka Hukumar Tace Finafinan zuwa ga Kananan Hukumomi 44 na Jihar. Ya kuma bayyana kudirin Gwamnatin Jihar na bunkasa cinikin sayar da finafinan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel