Abuja: Buhari ne ya kamata ya ziyarci Binuwai – In ji Shehu Sani

Abuja: Buhari ne ya kamata ya ziyarci Binuwai – In ji Shehu Sani

- Sanata Sani ya ce shugaba Buhari ya kamata ya ziyarci mutanen Binuwai, ba wai su ziyarce shi ba

- Sani ya bayyana cewa a al'adunmu a kasar Afrika mutane ke ziyarar ta’aziyya ba wai wanda aka yi wa rashi ba

- Sanatan ya ce shugaba Muhammadu Buhari ne kawai zai iya kawo karshen wannan kashe-kashen

Sanata Shehu Sani, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai a karkashin jam’iyyar APC ya bayyana cewa bai kamata a ce dattawan jihar Binuwai ne suka ziyarci shugaba Muhammadu Buhari a ranar Talata game da kashe-kashen da makiyaya suka yi wa ‘yan asalin jihar.

Ya ce a maimakon haka, shugaba Buhari ne ya kamata ya ziyarce su don yi musu ta’aziyya a kan rashin da suka yi.

Sanata Sani ya yi wannan magana ne a lokacin da yake jawabi a gidan telebijin na Channels a yau Laraba, 17 ga watan Janairu.

Abuja: Buhari ne ya kamata ya ziyarci Binuwai – In ji Shehu Sani

Sanata Shehu Sani, mai wakiltar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai

A cewarsa, ya kasance wata al'ada ce ta Afrika cewa lokacin da aka yi wa wani rasuwa, mutane ne ke ziyayar ta’aziyya ba wai wanda aka yi wa rashi ba.

KU KARANTA: Sheikh Dahiru Bauchi ya tofa albarkacin bakinsa kan rikicin makiyaya da manoma

Kamar yadda Legit.ng ke da labari, Sani ya jaddada cewa shugaba Buhari ya aika tawaga na musamman zuwa jihar Binuwai idan ba zai iya zuwa can da kansa ba.

Dan majalisar ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari ne kawai zai iya kawo karshen wannan lamarin.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel