Sanatan APC ya soki Buhari, ya zargi shugaban kasar da nada mutanen da basu cancanta ba

Sanatan APC ya soki Buhari, ya zargi shugaban kasar da nada mutanen da basu cancanta ba

Wani sanata daga jam’iyya mai ci wato APC, Sanata Isa Misau ya zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da nada mutane da basu cancanta ba a majalisar sa.

Sanatan na jihar Bauchi ya kuma bayyana cewa akwai son kai wajen nada Ahmed Abubakar a matsayin darakta janar na hukumar lekan asiri na kasa.

Ya yi zargin cewa Mista Abubakar ya fadi jarrabawar da ya gabata kafin a nada shi.

Shugaban kasa Buhari ya nada Mista Abubakar a matsayin shugaban hukumar leken asiri a ranar Laraba, 10 ga watan Janairu.

KU KARANTA KUMA: Kungiyar Miyetti Allah ta gabatar da muhimmin bukata a gaban shugaba Buhari

Misau ya bayyana cewa ba’a bi ka’ida ba wajen nada Mista Abubakar wanda a baya ya kasance babban mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin waje.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel