Kalaman Shugaba Trump ba su yi mana dadi ba – Onu

Kalaman Shugaba Trump ba su yi mana dadi ba – Onu

- Shugaba Donald Trump ya soki kasashen Afrika kwanakin baya

- Kalaman Trump sun jawo fushin wani Ministan kimiyyan kasar

- Dr. Ogbonoyya Onu yace kalaman Trump sam bai masu dadi ba

Mun samu labari cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta soki kalaman da Donald Trump yayi amfani da su a kan Kasashen Afrika wanda Najeriya tana cikin su.

Kalaman Shugaba Trump ba su yi mana dadi ba – Onu

Minsitan kimiyya na Najeriya Dr. Onu ya soki Trump

Ministan kimiyya da fasaha na Gwamnatin Buhari watau Dr. Ogbonnoya Onu yayi Allah-wadai da kalaman batancin da Shugaban na kasar Amurka Donald Trump yayi amfani da su. Onu ya bayyana wannan ne a Garin Abuja.

KU KARANTA: Gwamnatin Buhari tayi taron FEC na Majalisa

Dr. Onu ya bayyana cewa sun tabbatar da cewa akwai matsaloli a Najeriya amma Kasar ba ta wuce gyara ba. Onu yace nan gaba idan Najeriya ta gyaru, mutanen waje za su rika neman shigowa Najeriya domin su samu dama a Kasar.

Kalaman na Shugaban Amurka Donald Trump ya jawo ce-ce-ku-ce inda Kasashen Afrika su kayi ta sukar Shugaban kasar. Ba dai yau Donald Trump ya fara wannan katabora ba a Duniya, amma dai yayi wuf ya lashe aman na sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel