Kungiyar tsagerun Neja Delta ‘Avengers’ ta lashi takobin cigaba da karya tattalin arzikin Najeriya

Kungiyar tsagerun Neja Delta ‘Avengers’ ta lashi takobin cigaba da karya tattalin arzikin Najeriya

Sananniyar kungiyar tsagerun Neja Delta, ‘Avengers’ ta farfado daga sumar da tayi, inda ta sha alwashin zata cigaba da farfasa bututun mai,kamar yadda ta saba yi a baya, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito tsagerun sun bayyana haka ne a ranar Laraba 17 ga watan Janairu a shafin yanar su, inda suka ce sun kammala shirye shiryen fara kai hare haren:

KU KARANTA: Tsadar rayuwa da baƙin talauci ya sanya Magidanci hallaka iyalinsa gaba ɗaya, da shi kansa

“Wannan hare haren da zamu fara kaiwa, zai zamo mai tsananin hadari, kuma zamu karkata ne ga manyan kamfanonin mai.” Inji su.

Kungiyar tsagerun Neja Delta ‘Avengers’ ta lashi takobin cigaba da karya tattalin arzikin Najeriya

Kungiyar tsagerun Neja Delta

Wadannan tsagerun su ne wanda suka yi sanadiyyar raguwar gangan danyen mai da Najeriya ke hakowa a shekarar 2016, a yanzu ma sun lashi takobin kai hare hare a kan rijiyoyin mai dake Bonga Platform, Agbami, EA Field, Britania-U Field, Akpo Field.

Tsagerun sun cigaba da fadin “Muna shawartar masu rijiyan main a Egina FPSO dasu san na yi, don kuwa lallai cikin yan kwanaki kadan zai fuskanci fushin mu. A ranar 15 ga watan Janairu na 2018 ne aka cikashekaru 62 da gano mai a yankin Oloibiri, kuma a ranar ne muka gudanar da gagarumin taro.

“A taron ne muka yanke shawarar rikta rikita da kuma kashe kashen da mukaga yana faruwa a Najeriya a yanzu haka, hakan ne lokacin da yafi dacewa a sauya fasalin kasar nan.” In ji su.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel