Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama mutane uku kan tashin bam din Edo

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama mutane uku kan tashin bam din Edo

Rundunar yan sandan jihar Edo sun kama mutane uku dake da alaka da tashin bam din da ya yi sanadiyan mutuwar mutun daya a Okpella, karamar hukumar Etsako East dake jihar.

Kwamishinan yan sanda, Mista Johnson Kokumo, ya ambaci sunayen masu laifin a matsayin Idris Ibrahim, Zainab Ibrahim da kuma Oyeza Abdul.

Kokumo ya bayyana cewa wani daga cikin masu laifin, Idris Abdulmalik ya tsere.

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama mutane uku kan tashin bam din Edo

Yanzu Yanzu: Yan sanda sun kama mutane uku kan tashin bam din Edo

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisa na yau (hotuna)

Jami’an yan sandan sun kuma samo kayayyaki da dama wanda suka hada da gurneti, da sauran abubuwa daga mutane dake hada bama-baman.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel