Ana kokarin tsige Bukola Saraki saboda zargin canza sheka zuwa PDP – Sanata Misau

Ana kokarin tsige Bukola Saraki saboda zargin canza sheka zuwa PDP – Sanata Misau

Sanata Isa Hamma Misau, mai wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya a majalisan dattawa ya ce wani minista ne kan gaba wajen yunkuri da kaidin tsige shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki.

Misau ya bayyana hakan ne a filin majalisa yau Laraba yayinda ya ke magana akan rikicin makiyaya da manoma.

Sanatan ya ce akwai wasu yan tsiraru da ke shirin tsige shugaban majalisan bisa da zargin cewa yana shirin shekewa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP).

Ana kokarin tsige Bukola Saraki saboda zargin canza sheka zuwa PDP – Sanata Misau

Ana kokarin tsige Bukola Saraki saboda zargin canza sheka zuwa PDP – Sanata Misau

Yace: “Yayinda muke hutu, mutane da dama sun bi baya suna kokarin tsige shugaban majalisan dattawa. Wani minista ke kan gaba.

“Dalilin shine, sun ce shugaban majalisa zai bar APC saboda haka a zama masa cikas. Wani irin kasa ne wannan? "

KU KARANTA: Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya jagoranci zaman majalisa na yau (hotuna)

“Anyi nade-nade da yawa da ba bisa cancanta ba. Wasu miyagu sun kwace gwamnatin tamkar sun fi karfin shugaban kasa, kuma muce muna yaki da rashawa. Meyasa har yanzu ba’a kai Babachir Lawal kotu ba amma duk munyi shiru.”

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel