Yaki da ta'addanci: Rundunar tsaro ta hadin gwuiwa ta gudanar da wani muhimmin taro a Maiduguri

Yaki da ta'addanci: Rundunar tsaro ta hadin gwuiwa ta gudanar da wani muhimmin taro a Maiduguri

- Dakarun hukumar tsaron hadin gwuiwa sun gudanar da wani taro a Maiduguri

- An shirya taron ne domin tattauna yadda za'a kawo karshen aiyukan ta'addanci na kungiyar Boko Haram a kasashen dake gefen tekun Chadi

- Sun ci alwashin murkushe 'yan ta'addar kungiyar Boko Haram a kasashen gefen tekun Chadi

Dakarun jami'an tsaro na hadin gwiwa (JTF) sun yi wani taro a kan yadda zasu kawo karshen aiyukan ta'addanci a kasashen dake gefen tekun Chadi. Sun gudanar da taron ne jiya a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno, karkashin jagorancin Manjo Lucky Irabor da Janar Rogers Nicholas; shugaban rundunar soji ta Ofireshon Lafiya Dole mai aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar Borno.

Makasudin shirya taron shine domin a tattauna hanyoyin da za'a bi don tabbatar da zaman lafiya mai dorewa a kasashen gefen tekun Chadi da kuma yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Yaki da ta'addanci: Rundunar tsaro ta hadin gwuiwa ta gudanar da wani muhimmin taro a Maiduguri

Dakarun Rundunar tsaro ta hadin gwuiwa

Da yake magana yayin gudanar da taron, Manjo Janar Irabor ya ce "Muna yaki da 'yan ta'adda da kuma ta'addanci; ta'addanci da 'yan ta'adda basu basa girmama dangantakar dake tsakanin kasashe masu makwabtaka da juna, shi yasa ya zamar mana dole mu hada karfi da karfe ta fuskar musayar bayanai da zakulo sabbin hanyoyi yaki da 'yan ta'adda da aiyukan ta'addanci."

DUBA WANNAN: Shekau ya aike da sako ga iyayen 'yan matan Chibok a sabon bidiyo

Ya kara da cewar "Yayin da zaman lafiya ya fara dawowa a yankunan kasashen tekun Chadi dake fama da rigingimu, ya zama dole mu tabbatar da cewar aiyukan ta'addanci basu dawo ba yayin da jama'a suka koma harkokinsu na kasuwanci a tsakanin kasashen"

Kazalika, shugaban rundunar Ofireshon Lafiya Dole, Manjo Janar Nicholas, ya bayar da tabbacin hada kai da dakarun sojin hadin gwuiwar domin tabbatar da an kubutar da dukkanin mutanen da kungiyar Boko Haram ke garkuwa da su, da suka hada da 'yan matan Chibok da wasu ma'aikatan jami'an Maiduguri.

A yayin da ake ganin zaman lafiya ya fara samuwa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, sai gashi kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon faifan bidiyo inda take bayyana cewar tana nan daram a kan yakin da take yi da gwamnati.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel