Ba za mu gama aikin jirgin kasa a lokacin da mu ke sa rai ba – Amaechi

Ba za mu gama aikin jirgin kasa a lokacin da mu ke sa rai ba – Amaechi

- An fara samun matsala wajen aikin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan

- Ana sa ran za a kammala aikin hanyar zuwa karshen shekarar bana

- Sai dai Ministan sufuri Amaechi yace yanzu sun a fama da tasgaro

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta fara kukan cewa lokaci yana nema ya sha gaban su a game da wasu ayyuka da ake yi a cikin kasar.

Ba za mu gama aikin jirgin kasa a lokacin da mu ke sa rai ba – Amaechi

Lokaci yana kure mana inji Rotimi Amaechi

Ministan sufurin kasar Rotimi Amaechi ya nayyana cewa watakila ba za a kammala aikin jirgin kasan Legas zuwa Ibadan a lokacin da aka kayyade na karshen shekarar nan ba. A da ana sa ran za a karasa aikin a Disamban 2018.

KU KARANTA: Hannun jarin Najeriya yayi kasuwa a Duniya

Rotimi Amaechi yace sun fara samun cikas wajen aikin jirgin da ake yi daga Garin Legas zuwa Ibadan. Daga cikin matsalar da ake fuskanta akwai hanyoyin ruwa da gas da kuma gine-ginen da aka ci ma a kan hanyar da ake aikin.

Ya bayyana wannan ne bayan ya gana da mutanen Kasar Sin masu aikin. Yanzu dai lokaci na nema ya kurewa ‘Yan kwangilar. Amaechi yace za su yi kokarin hada-kai da Gwmnatocin Jihohi domin ganin sun shawo kan wadannan matsalolin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel