Gwamnati ta warewa ‘Yan kwangila Tiriliyan 1.2 na aiki a Najeriya

Gwamnati ta warewa ‘Yan kwangila Tiriliyan 1.2 na aiki a Najeriya

- An ware sama da Tiriliyan 1 na manyan ayyuka a shekarar bara

- Har gobe ana amfani ne da kasafin kudin shekarar bara a Kasar

- Ba a dabbaka kundin kasafin kudin bara sai karshen shekara ba

Mun samu labari cewa Gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta saki sama da Naira Tiriliyan 1.2 domin yin wasu manyan ayyuka a fadin kasar nan inji ofishin hada-hadar bashi a Najeriya.

Gwamnati ta warewa ‘Yan kwangila Tiriliyan 1.2 na aiki a Najeriya

Gwamnatin Buhari ta saki kudin manyan ayyuka

An rattaba hannu kan kasafin kudin bara ne a tsakiyar shekarar da ta wuce kuma daga lokacin zuwa karshen shekarar Gwamnatin Tarayya ta ware sama da Naira Tiriliyan da 'Yan kai guda na wasu manyan ayyuka da ake yi a kasar.

KU KARANTA: Gwamnatin tarayya za ta yiwa fursunoni 368 goma ta arziki

An saki kudin gina tituna da wasu ayyuka na Tiriliyan 1.254 wanda daga ciki an samu kudin ne ta tsarin Sukuk na Gwamnatin Shugaba Buhari. Jaridar Daily Trust tace za kuma a cigaba da sakin wasu kudin domin ayyuka a fadin kasar.

Har yanzu dai ana amfani ne da kasafin kudin bara kafin a sa hannu a kasafin kudin wannan shekarar. Kundin kasafin kudin kasar ya dauki dogon lokaci ne a Majalisa kafin a amince da shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel