Kaduna: Iyaye da 'yan makaranta sun nemi a kawo karshen yajin aikin malamai

Kaduna: Iyaye da 'yan makaranta sun nemi a kawo karshen yajin aikin malamai

- Iyaye da 'yan makaranta a jihar Kaduna sun nemi a kawo karshen yajin aikin malaman makarantun gwamnati

- Wasu yara a jihar sun koka cewa lamarin ya dame su ganin cewa abokaninsu a makarantu masu zaman kansu na ci gaba da karatu

- Wani iyaye ya ce, shaka babu akwai wasu daga cikin malamai marasa cancanta da basu san abin da aikin koyarwa ta kunsa ba

‘Yan makarantun firamare a jihar Kaduna da iyayensu sun yi kira ga malamai masu yajin aiki a jihar su kawo karshen wannan yajin saboda yaran talakawa ne kawai lamarin ya shafa.

Malaman makarantar firamare da na sakandare a jihar Kaduna a ranar 8 ga watan Janairun shekara ta 2018 sun fara wani yajin aiki marar iyaka don bayyana rashin amincewar su a kan kimanin malamai 22,000 wadanda aka yi zargin cewa sun kasa cin jarabawa ‘yan haji 4 na firamare wanda gwamnatin jihar ta gudanar don gwada kwarewar su.

Majiyar Legit.ng ta tabbatar cewa, tun lokacin da aka fara wannan yajin aikin yaran da ke halartar makarantun gwamnati ba su zuwa makaranta yayin da abokan su a makarantun masu zaman kansu suna ci gaba da karatu.

Kaduna: Iyaye da 'yan makaranta sun nemi a kawo karshen yajin aikin malamai

Gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai

Wani yaro mai shekaru bakwai da haifuwa da ke halartar makarantar firamare na Trikania, Musa Lawal wanda aka samu yana yawon bansa a titi a lokacin da ya kamata a ce yana makaranta, Lawal ya nuna bakin cikinsa game da yajin aikin da malamai suke yi, yana mai cewa, "Na yi fata a ce iyayena suna da kuɗi don aika ni zuwa makarantar masu zaman kansu don kada in sha wahala saboda rashin daidaito tsakanin gwamnati da malamai".

KU KARANTA: Sai mun hada kai sannan Najeriya zata ci gaba - Atiku

Wata daliba, Margaret wanda ta ke makaranta a Barnawa, ta koka cewa sakamakon yajin aiki yanzu ta koma sayar da ayaba don taimaka wa iyayenta tun lokacin da aka dakatar da su zuwa makaranta saboda yajin aikin.

Wani iyaye, Ibrahim Haruna, ya bayyana cewa wannan yajin aikin da malaman makaranta suka fara, ya jefa yaran talakawa cikin wani halin rashin abin yi da zaman kashe wando.

Ya yi kira ga malamai don su kawo karshen yajin aikin su kuma koma bakin aikinsu. "Na yi imani da cewa abin da gwamnati ke ƙoƙari ta yi shi ne ta kawo kyakyawar tsarin ilimi mai inganci a jihar saboda lalle akwai wasu malamai marasa cancanta da basu san abin da aikin ta kunsa ba".

Saboda haka ya yi kira ga bangarorin biyu da gwamnati da kuma kungiyar malamai na Najeriya (NUT) don tattaunawa da kawo ƙarshen yajin aikin saboda yaran talakawa au samu ilimi mai inganci.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel