Babban magana! Wasu 'yan Najeriya za su shiga yajin aikin kin sayen nama

Babban magana! Wasu 'yan Najeriya za su shiga yajin aikin kin sayen nama

- Wasu yan Najeriya na kira da al'umma su kauracewa cin naman sa domin nuna bacin ransu bisa hare-haren da ake zargin makiyaya da kaiwa a wasu sasan kasar

- Al'umman sun bayyana ra'ayin na su ne ta hanyar wata muhawarar bayana ra'ayi da jardiar Punch ta gudanar ta yanar gizo

- Sakamakon ya nuna 2,522 suna son kauracewa cin naman, 540 basu goyan baya, sai kuma 169 sun ce duk inda ta fadi dama ne

A yunkurin su na nuna bacin rai da kin amincewa da hare-haren da ake zargin makiyaya ke kaiwa a wasu sassan kasar na, wasu 'yan Najeriya suna kira ga al'umma sun kauracewa cin nama musamman na shanu da raguna.

Al'ummar sun bayyana wannan shawarar ta su a wani mahawarar jin ra'ayi da jaridar Punch ta gudanar ta kafar yanar gizo da aka fara a karfe 2.34 na yammancin Alhamis na makon da ya wuce kuma aka kammala jiya Talata.

Mahawarar jin ra'ayin ta tambaya baiwa al'umma zabi kamar haka; Wadanda ke goyon bayan kauracewa cin nama; Wadanda ba su goyon baya da kuma wadanda ba su damu ba ko a kaurace ko akasin hakan.

DUBA WANNAN: Bamu goyon bayan kafa filayen kiwo na makiyaya, inji mabiya darikar Katolika

Cikin mutane 2,961 da suka bayyana ra'ayoyin su a mahawarar, 2,252 suna son a kauracewa cin nama, 540 ba su goyi bayan kauracewa cin naman ba sai kuma 169 sun ce duk inda ta fada dama ne.

Wadanda suka goyi bayan kaurcewar galibi sun koka ne kan yadda ake ta kai hare-hare a sasan kasar nan kuma ana zargin makiyayan ne, wasu kuma suna son kauracewar ne saboda naman shanu na iya lahani ga dan adam musamman masu nisan shekaru.

Wanda kuma basu goyi bayan kauracewa cin naman ba sun ce naman na da mahimmanci wajen samar wa dan adam da sinadarin gina jiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel