Yanzu-Yanzu: EFCC ta gurfanar da Justice Yinusa kotu kan laifin cin hanci

Yanzu-Yanzu: EFCC ta gurfanar da Justice Yinusa kotu kan laifin cin hanci

- Hukumar EFCC ta gurfanar da mai shari'a Mohammed Yinusa a gaban kotu kan laifin cin hanci

- Hukumar ta zargi Yinusa a kan laifuka biyar tare da Esther Agbo, ma'aikaciyar kamfanin lauya na Rickey Tarfa (SAN)

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da mai shari'a, Mohammed Yinusa, a gaban babban kotun Legas wanda ke zaune a Ikeja.

Kamar yadda Legit.ng ke da labari , an tuhume mai shari'ar ne a kan laifuka biyar tare da Esther Agbo, ma'aikaciyar kamfanin lauya na Rickey Tarfa (SAN).

Lokacin da aka karanta musu laifukan, dukansu biyu ba su amince da zargin a gaban alkali ba, wanda mai shari'a Sherifat Solebo ta jagoranta.

Yanzu-Yanzu: EFCC ta gurfanar da mai shari'a Yinusa kotu kan laifin cin hanci

Zanga-zangar ki amincewa da ci cin hanci da rashawa a Najeriya

Laifi na farko, mai shari'a Yinusa ana zargin sa da ƙoƙari ya karkatar da tafarkin shari'a ta hanyar yin amfani da sadarwa sirri tare da Mista Rickey Tarfa, SAN a lokacin da ya ke sauraron shari’ar babban lauyoyi biyu.

KU KARANTA: Sanatoci ba su iya tunkarar Buhari da gaskiya saboda saboda tsoron kujerunsu – Shehu Sani

Na biyu, an zargi Yinusa da laifin cin hanci da rashawa saboda zargin cewa ya karbi N1.5 miliyan a hannu wanda ake zargin su tare, Esther Agni don yanke hukuncin da zai ba kamfanin lauya na Rickey Tarfa nasara a shari’ar.

Laifi na uku, an samu mai shari'a Yinusa da laifin amincewa da samun tallafin kudi daga wani babban lauya, Mista Joseph Nwobike (SAN) don yanke hukuncin da zai baiwa shari’ar lauya da ke gabansa nasara.

Na hudu, EFCC ta yi zargin cewa mai shari'a Yinusa ya karbi dubu N750,000 daga Mista Nwobike da kuma laifi na biyar, Esther Agbo ne ake zargi da bayar da cin hanci NI.5 miliyan zuwa ga Justice Yinusa domin ta jawo hankalinsa waje yanke hukuncin da zai ba kamfanin lauya na Rickey Tarfa nasara a shari’ar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel