Shittu ya zargi Ajimobi da nuna bangaranci da raba kawunan yan APC a jihar Oyo a wasikar da ya rubutawa Buhari

Shittu ya zargi Ajimobi da nuna bangaranci da raba kawunan yan APC a jihar Oyo a wasikar da ya rubutawa Buhari

- Ministar Sadarwa ya kai karar Tinibu, Ajimobi da Oyegun wajen Buhari

- Shittu yace Ajimobi ya fushi da shi saboda ya bayyana ra'ayin na tsayawa takararn gwamnan jihar Oyo a zaben 2019

Adebayo Shittu, ministan sadarwa, ya kai karar gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi, John Odigie-Oyegun, da jagoran APC, Bola Ahmed Tinubu, wajen shugaban jam’iyyar wajen shugaban kasa, Muhammadu Buhari a wata wasika da ya rubuta masa.

A wasikar, Shittu ya zargi gwamnan jihar Oyo, da nuna bangaranci, girman kai, da raba kawunan mambobin jam’iyyar APC a jihar Oyo dan rage ma wasu karfi a jam’iyyar.

Shittu ya zargi Ajimobi da nuna bangaranci da raba kawunan yan APC a jihar Oyo a wasikar da ya rubutawa Buhari

Shittu ya zargi Ajimobi da nuna bangaranci da raba kawunan yan APC a jihar Oyo a wasikar da ya rubutawa Buhari

Adebayo Shittu ya zargi gwamnan da ba da umarnin rusa cibiyar rubuta jarabawa na kwamfuta wanda ake kan ginawa.

KU KARANTA : Hukumar SSS ta gayyaci wani mallamin addinin Krista ofishin ta akan sukar Buhari da yayi

Shittu yace gwamnan yana fushi da shi, saboda ya karbi sarautan da Olubadan ya bashi da kuma bayyana ra’ayin sa na tsayawa takaran gwamnan jihar Oyo a zaben 2019 da zai yi.

Adebayo yace babu wata gaba tsakanin sa da gwamna Ajimobi, amma ya yana tunatar da shi kada ya rusa jam’iyyyar da ta kawo shi kan mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel