Rundunar soji zata canja tsarin tura dakarunta yankin Arewa maso gabas – Inji Buratai

Rundunar soji zata canja tsarin tura dakarunta yankin Arewa maso gabas – Inji Buratai

Shugaban hafsan sojin Najeriya, Leftanal janar Tukur Buratai, ya bayyana shirye-shiryen rundunan sojin Najeriya kan sake tsarin tura sojoji zuwa yankin arewa-maso-gabas.

Buratai ya bayyana haka ne a ranar Talata yayinda yake karban bakuncin kwamitin dake wakiltan rundunan soji a hidikwatan rundunan a Abuja, babban birnin tarayya.

A cewarsa, matakin ya zama dole don tabbatar da cewa rundunan sun samu sakin jiki yayinda suke gudanar da aikinsu. Wannan sake tsare-tsaren har ila yau zai hada da raguwa a adadin gine-gine na tare mahara.

Ko da yake shugaban rundunan bai bayyana muhimmancin kan matakan ba akan yaki da ta’addanci ba a yankunan da al’amarin ya shafa, ya ce za’a soma sake tsare-tsaren idan aka sa hannu a kasafin kudin 2018.

Rundunar soji zata canja tsarin tura dakarunta yankin Arewa maso gabas – Inji Buratai

Rundunar soji zata canja tsarin tura dakarunta yankin Arewa maso gabas – Inji Buratai

Kafin a shirya tsare-tsaren wajen tura rundunan, Buratai ya roki da ayi kari kan kudaden rundunar.

KU KARANTA KUMA: Ku zamo masu hakuri a tsakaninku – Sakataren tarayya ga yan Najeriya

A bangarensa, shugaban kwamitin majalisa kan rundunan sojin Najeriya, Rimamande Kwewum, ya ce majaliar dokoki tana sane da kalu bale da hukumar tsaron take fuskanta na kudade kuma zata yi gwargwadon kokarinta na ganin an samu hanyoyi, kamar yanda yake tsare a kundin mulki, na samar ma Karin kudade ga rundun ar sojin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel