An tsaurara matakan tsaro a sansanin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky

An tsaurara matakan tsaro a sansanin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky

An tsaurara matakan tsaro a Unity Fountain dake Abuja bayan da wata kungiya ta fara dirshan domin neman sakin shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi da aka fi sani da shi'a, Ibrahim El-Zakzaky.

Daruruwan mambobin kungiyar, Concerned Nigerians, da kuma dubban magoya bayan malamin ne suka yi dandazo a wurin zanga-zangar. shugaban kungiyar Concerned Nigerians, Deji Adeyanju, ke jagorantar zana-zangar, yayin da mawaki, Charly Boy, ke mara masa baya.

Masu zangar-zangar na bukatar gwamnatin Najeriya ta gaggauta sakin El-zakzaky daga kamun da hukumar jami'an tsaron farin kaya (DSS) ta yi masa tun watan Disambar 2015. Kazalika masu zangar-zangar na bukatar gwamnati ta kawo karshen kashe-kashe tsakanin makiyaya da manoma a fadin kasa bakidaya.

An tsaurara matakan tsaro a sansanin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky

An tsaurara matakan tsaro a sansanin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky

Da yake magana a wurin taron zanga-zangan, adeyanju, ya yi kira ga shugaba Buhari da ya yi biyayya ga umarnin kotu, ya saki El-zakzaky, tare da kara yin kira ga jami'an tsaron Najeriya da su daina tsangwamar mabiya shi'a.

DUBA WANNAN: Dalilin da ya sa muka dauki tsauraran matakai domin ganin Jammeh ya sauka - Buhari

An tsaurara matakan tsaro a sansanin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky

An tsaurara matakan tsaro a sansanin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky

Charly Boy, da yake tofa albarkacin bakinsa cikin Turancin fijin, ya ce ya kamata gwamnati ta gaggauta kawo karshen tsangwama da jami'an tsaro ke yiwa 'yan Najeriya, sannan ya bukaci a gaggauta sakin El-Zakzaky, yana mai bayyana cewar halayen shugabannin Afrika na danniya da rashin mutunta bil'adama ya jawo ake raina mu a duniya, har take kaiwa ga wasu shugabannin duniya suke kalaman cin fuska ga nahiyar.

An tsaurara matakan tsaro a sansanin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky

An tsaurara matakan tsaro a sansanin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky

An tsaurara matakan tsaro a sansanin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky

An tsaurara matakan tsaro a sansanin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky

Legit.ng ta rawaito maku, a daya daga cikin labaranta, cewar kungiyar ta bayyana cewar za ta fara zaman dirshan na sai baba-ta-gani a unity Fountain ranar 17 ga watan Janairu. Shugabannin kungiyoyin kare hakkin bil'adama da dama sun bayyana niyyar su ta marawa zanga-zangar baya, daga ciki harda fitaccen lauya Femi falana da Obiageli Ezekwesili, tsohuwar ministar ilimi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel