Bamu goyon bayan kafa filayen kiwo na makiyaya, inji mabiya darikar Katolika

Bamu goyon bayan kafa filayen kiwo na makiyaya, inji mabiya darikar Katolika

- Kungiyar Bishof 'yan darikar Katolika sun nuna kin amincewar su ga kudirin gwamnatin na kafa filayen kiwo ga makiyaya

- Kungiyar ta ce a maimakon hakan, kamata yayi a taimaka wa makiyayan su gina gidajen gona kamar yadda kasashen da suka cigaba ke yi

- Kungiyar ta mika ta'aziyar ta ga iyalan wanda suka rasu, ta kuma yi addu'an samun sauki ga wandanda suka jikkata

Kungiyar Bishof-Bishof na darikar Katolika na Najeriya (CBCN) ta yi kira da Gwamnatin Tarayyah ta yi watsi da kudirin ta na gina filayen kiwo a wasu jihohin domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai.

Wannan kirar ya fito ne cikin wata sako mai dauke da sa hannun Shugaban Kungiyar ta CBCN kuma Babban Bishof na garin Jos, Ignatus Kaigama da kuma Bishof din garin Gboko Rabaran William Avenya.

Bamu goyon bayan samar da filayen kiwo ga makiyaya - CBCN

Bamu goyon bayan samar da filayen kiwo ga makiyaya - CBCN

KU KARANTA: An tsaurara matakan tsaro a sansanin masu zanga-zangar neman a saki El-Zakzaky

Kazalika, Kungiyar ta nuna takaicin ta ga yadda laifukan garkuwa da mutane da wasu laifuka ke kara yaduwa a kasar nan, ta yi kira da gwamnati ta dauki matakin da ya dace kuma cikin gagawa.

"Abin da ya dace shine gwamnati ta samar da wani mafita a kan lamarin a maimakon ware filaye domin kiwo na makiyaya a jihohin kasar nan. Kamata ya yi gwamnati ta shawarci makiyayan su gina gidajen gona kamar yadda akeyi a kasashen da suka cigaba," inji Kungiyar

Kungiyar kuma ta mika ta'aziyar ta ga iyalan wadanda suka rasa rayukan su kuma ta yi addu'an samun sauki ga wadanda suka jikkata. Ta ce idan gwamnatin bata mike tsaye ta kare rayuka da dukiyoyin al'umma ba, hakan zai tilasta wa al'umma daukan makamai domin kare kansu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel