Sanatoci ba su iya tunkarar Buhari da gaskiya saboda saboda tsoron kujerunsu – Shehu Sani

Sanatoci ba su iya tunkarar Buhari da gaskiya saboda saboda tsoron kujerunsu – Shehu Sani

Shehu Sani, sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa y ace wasu abokan aikinshi bas u iya fuskantar Buhari da gaskiya a kan kashe-kashen da ke faruwa saboda suna son su dawo a 2019.

Sani ya bayyana wannan ne ranan Talata a filin majalisa yayinda yake magana a kan rahoton kwamitin tsaron.

Ya ce a maimakon fadin gaskiya a kan abubuwan da ke faruwa a kasa, wasunsu fadanci suke kawai.

Sanatan ya kara da cewa yan Najeriya sun debe tsammani daga gwamnati.

Sanatoci ba su iya tunkarar Buhari da gaskiya saboda saboda tsoron kujerunsu – Shehu Sani

Sanatoci ba su iya tunkarar Buhari da gaskiya saboda saboda tsoron kujerunsu – Shehu Sani

Yace: “Ya kai matuka yanzu mutane sun debe tsammani daga gwamnati. Muna ta kankanba maimakon fadin gaskiya. Bamu son fuskantar fadan shugaban kasa da shugaban kasa saboda muna burin dawowa majalisa,”

“Ba su son rasa kujerarsu amma mutane na mutuwa a kasar nan. Ku yi hakuri.”

KU KARANTA: Wani shu'umin matsafi da ya kashe 'yan sanda biyu ya gamu da fushin sojojin Najeriya

Sanatan ya ce wannan lokaci ne da ya kamata shugaban kasa ya bayyana shugabanci.

Yace: “Abinda ke birgeni da fadar shugaban kasa shine idan lokacin sukan majalisan dokoki, basu sassautawa.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel