Kisan dan majalisa: Gwamnati ta sanya dokar hana fita a Takum

Kisan dan majalisa: Gwamnati ta sanya dokar hana fita a Takum

- An kara matakan tsaro a garin Takum dake jihar Taraba

- Gwamnatin ta Taraba ta sanya dokar hana fita bayan kisan dan majalisa da masu garkuwa suka sace

- A watan Disamba ne masu garkuwa suka sace dan majalisan

An tura karin jami’an tsaro zuwa yankin Takum domin ganin ba'a karya doka ba duk da dokar hana fita da aka sanya a garin.

An tattaro cewa gwamnatin jihar ta kafa matakan tsaro, don tsammanin karya doka dake iya aukuwa bayan kisan wani dan majalisa mai wakiltan mazabar Takum a majalisan dokokin jihar, Mista Hosea Ibi wanda masu garkuwa da mutane suka kashe bayan sun amshi kudin fansa naira miliyan 25.

An tattaro cewa, matasan Kuteb, sunyi barazanar yin zanga-zanga kan kisan dan majalisan kuma sakamakon haka ne gwamnatin jihar ta kafa dokar hana fita.

An tsinci gawar dan majalisan wanda aka yi garkuwa da shi a gidan mahaifiyarsa a ranar 30 ga watar Disamba 2017 a Takum ne a ranar Litinin a wani jeji dake tsakankanin Jihohin Taraba da Benue.

Kisan dan majalisa: Gwamnati ta sanya dokar hana fita a Takum

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku

An tattaro cewa matasan suna zargin mambobin sanannen mai garkuwa da dan fashi da makami mai suna Ghana daga jihar Benue da kasancewa mai hannu cikin kisan dan majalisan.

KU KARANTA KUMA: Wani Sanatan Katsina ya gargadi Buhari akan kafa burtalin makiyaya a jihohi

Yayinda yake bayyana ra’ayinsa, gwamna Darius Ishaku yayi Allah wadai da kisan Hosea Ibi, ya kuma sha alwashin cewa wadanda ke da hannu cikin kisan zasu fuskanci hukunci.

Har ila yau Gwamnan ya ziyarci gidan dan majalisan ya kuma mikawa iyalen dan majalisan ta’aziyyarsa.

A wani al’amari makamancin haka, kakakin majalisan dokokin jihar Mista Abel Oeter Diah ya jagoranci mambobin majalisar dokokin jihar zuwa jajenta iyalen dan majalisan.

Ministan harkokin mata, Hajiya Jummai Alhassan, ta bayyana kisan Ibi a matsayin rashin imani.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel