Ka binciko wadanda suka kai hare-hare a Benuwe cikin kwanaki 14: Majalisa ta fadawa Sifeta Janar

Ka binciko wadanda suka kai hare-hare a Benuwe cikin kwanaki 14: Majalisa ta fadawa Sifeta Janar

- Majalisar Dattawa ta dibar wa Sifeta Janar na rundunar kwanaki 14 domin zakulo wadanda ke da hannu cikin hare-haren Benuwe

- Kwamitin ta cin ma wannan matsayan ne bayan duba rahotonni daga jihar ta Benuwe

- Rahotannin sun bada shawarar a sake inganta hukumomin tsaro da ke fadin kasar nan domin kiyaye lafiya da dukiyoyin al'umma

Majalisar Dattawa ta bawa Sifeta Janar na rundunar yan sandan Najeriya Mista Ibrahim Idris wa'adin kwanaki 14 domin ya gudanar da bincike kana ya kamo wandanda ke da hannu cikin hare-hare da aka kai a jihar ta Benuwe wanda yayi sanadiyar rasa rayyuka da dukiyoyi.

Ka binciko wadanda suka kai hare-hare a Benuwe cikin kwanaki 14: Majalisa ta fadawa Sifeta Janar

Ka binciko wadanda suka kai hare-hare a Benuwe cikin kwanaki 14: Majalisa ta fadawa Sifeta Janar
Source: Depositphotos

An dauki wannan matakin ne bayan yin la'akari da rahoton kwamitin 'yan Majalisar na Dattawa garambawul ga harkokin tsaro a Najeriya wanda ya zama dole saboda halin rashin tsaro da sasan kasar da dama ke fuskanta.

KU KARANTA: Hukumar EFCC ta gurfanar da dan tsohon gwamna saboda cuwa-cuwan N92m

Ciyaman din kwamitin, Senata Ahmed Lawan na ya gabatar da rahoton a Majalisar rannan Talata.

Ya kara da cewa sauran shawarwarin da kwamitin ta bayar sun hada da nazari, garambawul da inganta hukumomin tsaro na kasar domin tabbatar wa dukkan garuruwan da ke kasar nan sun sami tsaro ingantace da suke bukata.

Lawan ya cigaba da cewa wata karin shawara da kwamitin ta bayar shine kiran taron gagawa na 'yan Majalisar domin kara duba hanyoyin da za'a tabbatar da tsaro da kuma hadin kan Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel