Wani Sanatan Katsina ya gargadi Buhari akan kafa burtalin makiyaya a jihohi

Wani Sanatan Katsina ya gargadi Buhari akan kafa burtalin makiyaya a jihohi

- Sanata mai wakiltan mazabar kuddancin Katsina ya gargadi shugaban kasa bisa tsawwalawa jihohi yankunan dabbobi

- Abu Ibrahim ya ce jihohi ne ya kamata su yanke shawarar kafa yankunan dabbobi

- Har ila yau ya gargadi hukumomin tsaro da jami’ansu da su kara kuzari wajen aiki don kare rayuka da kaddarorin yan Najeriya

Wani dan majalisa ya shawarci shugaban kasa Muhammadu Buhari akan tswwalawa gwamnonin jihohi da su kafa yankunan dabbobi.

Sanatan mai wakiltan mazabar yankin Kuddancin Katsina, Abu Ibrahim, ya ce dole kafa yankunan dabbobi ya kasance shawarar jihohi.

Ibrahim wanda ya lashe kujerar a karkashin jam’iyyar APC ya ce kafa yankunan dabbobi, hanyoyin kiwo da fulotan kiwon dabbobi abun muhimmi ne ga jihohi ba manufa ne wanda kasa da gwamnatin tarayya zata aiwatar ba.

Wani Sanatan Katsina ya gargadi Buhari akan kafa burtalin makiyaya a jihohi

Wani Sanatan Katsina ya gargadi Buhari akan kafa burtalin makiyaya a jihohi

A wani hira tare da jaridar Leadership, sanatan yayi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya mayar da hankali ga lamarin tsaron Najeriya don kawo karshen kashe-kashe a kasar.

KU KARANTA KUMA: An yiwa Najeriya jan fenti da jini – Kakakin majalisa Dogara ya yi korafi kan kisan Benue

Har ila yau ya lura cewa hukumomin tsaro da jami’ansu basu aiki sosai wajen kare rayuka da kaddarorin yan Najeriya

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel