An yiwa Najeriya jan fenti da jini – Kakakin majalisa Dogara ya yi korafi kan kisan Benue

An yiwa Najeriya jan fenti da jini – Kakakin majalisa Dogara ya yi korafi kan kisan Benue

- Kakakin majalisar wakilai yayi gargadi akan cigaba da kashe-kashe da makiyaya ke yi a fadin kasar

- Yakubu Dogara ya ce an yiwa Najeriya shafe da jinin Al’umma

- Kakakin majalisar wakilai ya bukaci shugaba Muhammadu Buhari da ya dauki matakai masu tsauri kan ma’aikata wadanda basu gudanar da ayyukansu

Kakakin majalisan wakilai, Yakubu Dogara, yayi gargadi cewa duk masu hannu a kashe-kashe da ake yi a fadin kasar Najeriya zasu fuskanci hukunci.

Dogara ya lura cewa babu mafaka ga masu aikata wannan irin laifin a kasar.

Yayinda yake gabatar da jawabi a majalisa a ranar Talata, 16 ga watan Janairu, Dogara yayi kira ga gwamnati a dukkan matakai da su kare yan Najeriya sannan kada su yarda kungiyoyi su daukaka rashin zaman lafiya kan mutane.

An yiwa Najeriya jan fenti da jinni – Kakakin majalisa Dogara ya yi korafi kan kisan Benue

An yiwa Najeriya jan fenti da jinni – Kakakin majalisa Dogara ya yi korafi kan kisan Benue

Har ila yau yayi gargadi ga shuwagabanni da su saki wasan daurawa juna laifi da suke yi su kuma mayar da hankali kan rayuka da kaddarorin mutane da suka zabesu.

KU KARANTA KUMA: Bamu amince a kirkiri burtali domin makiyaya ba a gonakin mu - Dattijan jihan Benuwe suka fadawa Buhari

Daga kashe-kashen wulakanci a jihar Rivers, zuwa kisa da ya zama ruwan dare a Benue, Taraba, Kaduna, Zamfara, Adamawa, Edo da sauran jihohin; anyi ma kasarmu jan fenti da jinin wadanda basu da alhakkin kowa.

Shugaban majalisan ya cigaba da buktar shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya dauki matakai masu tsauri akan ma’aikata wadanda basu gudanar da ayyukansu ga mutanensu.

Ya ce idan gwamnatin Tarayya ta sanya kokari zata iya magance kashe-kashe da makiyaya ke daukakawa a Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel