Majalisar dinkin Duniya ta daura nauyin binciken kashe kashe a wuyan wani haziƙin ɗan Najeriya

Majalisar dinkin Duniya ta daura nauyin binciken kashe kashe a wuyan wani haziƙin ɗan Najeriya

Karamin babban magatakardan majalisar dinkin duniya mai kula da ayyukan kwantar da tarzoma da tabbatar da zaman lafiya a Duniya, Jean-Pierre Lacroix ya nada wani dan Najeriya, Chikadibia Obiakor a matsayin wanda zai binciki kisan kiyashi da aka yi ma yan kasar Burundi a kasar Congo.

Shi da wannan dan Najeriya, tsohon soja ne wanda ya kai mukamin laftanar janar kafin yayi murabus, kuma kaakakin sakataren majalisar dinkin Duniya, Stephane Dujarric ne ya sanar da haka a ranar Talata16 ga watan Janairu a shelkwatar majalisar dake Newyork, Amurka.

KU KARANTA: Da ɗumi ɗumi: Hukumar EFCC ta turke tsohon gwamnan jihar Filato a Abuja

Premium Times ta ruwaito akalla yan kasar Burundi dake gudun hijira a Congo su 35 ne suka rasa rayukansu a hannu jami’an tsaron kasar Congo, sa’anann daruruwa suka samu rauni, ana zargin jami’an tsaron sun aikata haka ne a sansanin yan gudun hijira dake Kamanyalo, a ranar 15 ga watan Satmbar 2017.

Majalisar dinkin Duniya ta daura nauyin binciken kashe kashe a wuyan wani haziƙin ɗan Najeriya

Obiakor

Sai dai jami’an tsaron kasar Congo sun musanta zargin kisan da gangan, inda suka ce yan gudun hijiran ne suka shirya wata gagarumar rikici ne don nuna bacin ransu da wasu mutanensu guda biyu da aka kama suna hada makamai, a sakamakon kokarin kashe wutan rikicin ne mutane da dama suka mutu.

Majiyar Legit.ng ta kara da cewa aikin binciken ya kunshi bin diddigi kalubalen da hukumar tabbatar da zaman lafiya na majalisar dinkin duniya a kasar Congo ke fuskanta, musamman wajen gudanar da ayyukanta na tabbatar da tsaron fararen hula da kuma walwalar Sojojinta.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel