Rikicin Benuwe: Shugabannin majalisar Dattawa sunyi takakkiya zuwa fadar shugaban kasa

Rikicin Benuwe: Shugabannin majalisar Dattawa sunyi takakkiya zuwa fadar shugaban kasa

- Kashe-kashen jihar Benuwe ya tayar da maganganu da dama a majalisar dattawa

- A jiya Talata majalisar ta samar da wasu shawarwari da zai kawo karshen rikicin

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi shawarwari daga hannun shugabannin majalisar dattawa, karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki lokacin da sukayi takakkiya zuwa fadar da daren Talata,16 ga watan Junairu.

Rikicin Benuwe: Shugabannin majalisar Dattawa sunyi takakkiya zuwa fadar shugaban kasa

Rikicin Benuwe: Shugabannin majalisar Dattawa sunyi takakkiya zuwa fadar shugaban kasa

Kafin zuwansu fadar, sun dau wadannan matakai a filin majalisa:

1. A baiwa Sifeto Janar na yan sanda kwanaki 14 domin damke wadanda suka aikata wannan ta’asa

2. A umurci ma’aikatar aikin noma ta samar da kayayyakin da zai taimakawa ma’aikatanta wajen rijista matafiya a boda

KU KARANTA: Matasan Gari sun yi Babban Lauya Mike Ozekhome ihu a Legas

3. A fara tunanin samar da yan sandan jiha

4. Gwamnatin tarayya ta mayar da hankalin wajen samar da isasshen tsaro a kasa

5. Majalisar dattawa ta shirya taron tsaro na kasa

6. Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ana kyakkyawan lura da yan gudun hijra

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel