An bankado wata sabuwar badakalar Naira 460 biliyan a kasafin kudin Buhari na 2018

An bankado wata sabuwar badakalar Naira 460 biliyan a kasafin kudin Buhari na 2018

Wata kungiya wadda ba ta gwamnati ba da ke rajin tabbatar da mulkin adalci a Najeriya mai suna Centre for Social Justice ta sanar da bankado wata irin badakalar ayyukan boge da adadin kudin su ya tasar ma Naira biliyan 460 a kasafin kudin 2018.

Wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwar da kungiyar ta fitar ta hannun shugaban ta Mista Eze Onyekpere da kuma ya rarrabawa manema labarai a jiya.

An bankado wata sabuwar badakalar Naira 460 biliyan a kasafin kudin Buhari na 2018

An bankado wata sabuwar badakalar Naira 460 biliyan a kasafin kudin Buhari na 2018

Legit.ng ta samu cewa shugaban kungiyar ya bayyana cewa biyo bayan zaman binciken kwakwaf na kuma tsanaki da suka yi wa kasafin kudin na wannan shekarar sun gano wasu abubuwan da basu dace ba ko kadan a ciki da kuma basu da wani alfanu ga cigaban kasar nan.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa a watannin karshe na shekarar da ta gabata ne dai shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin gwamnatin tasa a gaban majalisar tarayyar Najeriya domin amincewa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel