Ku mayar da hankali al’amuran addini ba siyasa ba – Fadar shugaban kasa ga kungiyar CAN

Ku mayar da hankali al’amuran addini ba siyasa ba – Fadar shugaban kasa ga kungiyar CAN

- Fadar shugaban kasa ta yi raddi ga kungiyar Kiristocin Najeriya

- Kugiyar CAN tayi zargin cewa akwai hadin baki tsakanin gwamnati da makiyaya

A daren Talata, 16 ga watan Junairu, fadar shugaban kasa ta mayar da martani ga sakataren kungiyar mabiya Kirista to fuskanci al’amuran addininsu ba siyasa ba

Fadar shugaban kasa ta musanta zargin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya saba wasu bangarorin kudin tsarin mulkin Najeriya.

Mai mahgana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu, ya saki wannan jawabi ne a Abuja yayinda yake martani a kan maganar sakataren kungiyar CAN, Musa Asake, wanda yace shugaba Buhari ya saba kundin tsarin mulkin Najeriya.

Ku mayar da hankali al’amuran addini ba siyasa ba – Fadar shugaban kasa ga kungiyar CAN

Ku mayar da hankali al’amuran addini ba siyasa ba – Fadar shugaban kasa ga kungiyar CAN

Garba Shehu yace: “An jawo hankalinmu akan wani hira da manema labarai da sakataren kungiyar CAN, Dakta Musa Asake, yayi inda kalubalanci wasu abubuwa da gwamnatin shugaba Buhari tayi."

“ Abun takaicin shine bai iya kawo wani hujjan cewa an saba dokan kasa ba. Shugaba Buhari bait aba zama cikas ga demokradiyya ko kundin tsarin mulki ba."

KU KARANTA: Boko Haram tayi asarar manyan mayaka 2 a yayin artabun su da sojin Najeriya

“Babu wani wuri da aka saba dokar kasa kuma ba za’a taba samu karkashin wannan shugabancin ba. Kawai ya mayar da hankali harkan addini ya bar siyasa gay an siyasa.”

Za ku tuna cewa a jiyan kungiyar CAN ta ce tana zargin akwai hadin baki tsakanin gwamnati, jami'an tsaro da kuma makiyaya akan kashe-kashe da akeyi a jihar Taraba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a

Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da Kuma

Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel