Fashewar bam ya halaka mutum daya a Edo – In ji gwamnatin jihar

Fashewar bam ya halaka mutum daya a Edo – In ji gwamnatin jihar

- Gwamnatin Edo ta ce fashewar bam ya halaka mutum daya a jihar

- Gwamnatin ta bayyana cewa ta gano kayan aiki wanda ake hada bama-bamai a yankin karamar hukumar Etsako ta gabas

- Gwamnan ya ce ba zai zuba ido irin wannan na faruwa ba tare da ya dauki matakin magance su ba

Wani rahoto da gwamnatin jihar Edo ta fitar ta ce fashewar bam ya kashe wani mutum a jihar a ranar Litinin, 15 ga watan Janairu.

Sanarwar da ya fito daga fadar gwamnatin jihar da ke birnin Benin, a ranar Talata ta bayyana cewa fashewar ya faru ne a garin Okpella, a yankin karamar hukumar Etsako ta gabas.

Sanarwar ta ce an kuma gano kayan aiki wanda ake hada bama-bamai a yankin.

Fashewar bam ya halaka mutum daya a Edo – In ji gwamnatin jihar

Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki

An yi tashin hankali a kwanan nan a Okpella saboda wani rikici tsakanin kamfanin Obu Ciment da Kamfanin Dangote Group game da mallakar wani filin hakar ma'adinai a yankin.

KU KARANTA: Mabiya akidar shi’a sun ƙirƙiro sabon salon yin mubaya’a ga Ibrahim El-Zakzaky

Idan dai baku manta kimanin makonni biyu da suka wuce Legit.ng ta ruwaito cewa gwamnatin jihar ta ce, wasu 'yan bindiga sun kai hari ga tawagar motocin gwamna Godwin Obaseki a Okpella, wanda aka yi zargin cewa babban darakta na kamfanin Obu Ciment yana da hannu a lamarin, Yusuf Binji. Amma, hukumar 'yan sandan jihar ta ce ba ta san da harin ba.

Mista Obaseki a ranar Talata ya umarci 'yan sanda da jami'an tsaro na SSS, su binciko kayan fasewa da saura makamai a Okpella, da kuma kwance damarar yaki daga ‘yan bindiga a yankin.

"Ba za mu iya ɗauka cewa abubuwa suna tafiya yadda ya kamata ba. Dole ne mu kwace makamai daga hannun mutane masu zaman kansu a cikin wannan yanki, kuma mu tabbatar da zaman lafiya a wannan yanki", in ji Mr. Obaseki a matsayin mai magana yayin da ya ke gaya wa sarkin Okpella, Andrew Dirisu, wanda ya jagoranci sauran shugabannin yankin a ziyarar girmamawa ga gwamnan.

"Mai martaba, idan ba saboda fashewar da ya faru a garin ba inda mutum daya ya mutu, ba ku da masaniyar cewa akwai irin wannan kayan fasewa a hannun mutane a yankinku" ,in ji gwamnan.

Gwamnan ya ce ba zai zuba ido irin wannan na faruwa ba tare da ya dauki matakin magance su ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel