Matasan Gari sun yi Babban Lauya Mike Ozekhome ihu a Legas

Matasan Gari sun yi Babban Lauya Mike Ozekhome ihu a Legas

- Lauyan da ke kare Uwargidan Jonathan ya sha kunya a gaban Jama’a

- An rika yi wa Mike Ozekhome ihu barawo-barawo a wajen wani taro

- Babban Lauyan Kasar yace ba fa zai daina shiga Kotu da Gwamnati ba

A cikin 'Yan kwanakin nan ne Lauyan da ke kare Matar tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan watau Patience ya sha kunya a gaban jama'a wajen wani taro a Legas inda aka rika kiran sa Ole-Ole!

Matasan Gari sun yi Babban Lauya Mike Ozekhome ihu a Legas

Wasu Lauyoyi na ke kare manyan barayi a Najeriya

Kamar yadda Sahara Reporters ta fitar da bidiyo an ga yadda mutanen Gari su ka rika yi wa babban Lauyan kasar ihu ana tir da shi wajen wani taro da aka saba shiryawa a kowace shekara don tunawa da tsohon Lauya Gani Fawehimi.

KU KARANTA: An rantsar da sababbin Kwamishinoni a Jihar Sokoto

Shi dai Lauyan Mike Ozekhome SAN ya maida martani ga Matasan da su ka rika yi masa ihun barawo a Garin Legas inda yake cewa ba zai fasa shiga Kotu da Gwamnatin Tarayya ta APC ba inda yake ba ta kashi a gaban shari'a a cewar sa.

Mike Ozekhome shi ne Lauyan da ke kare Patience Jonathan bisa zargin da ake yi mata na mallakar Miliyoyin daloli da Biliyoyin Naira ta hanyar da ba ta dace ba. Kwanan nan ya sha kashi a gaban Kotu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel