Wani matashi ya rasa ransa a sanadiyyar shiga tsakanin wasu yan giya dake faɗa

Wani matashi ya rasa ransa a sanadiyyar shiga tsakanin wasu yan giya dake faɗa

Rundunar Yansandan jihar Enugu ta sanar da cafke wan mahauci mai suna Michael Kingsley kan tuhumarsa da laifin kisan kai, wanda suke zargi ya hallaka abokin aikinsa, Ifeanyi Egwuagu.

Kaakakin rundunar,SP Ebere Amaraizu ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace hakan ya auku ne a unguwar Ogui ne jihar, ranar 14 ga watan Janairu, da misalign karfe 10:30 na dare, inj rahoton Daily Trust.

KU KARANTA: Gwamnati ta yi rusau a gidan Uwargidar tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan

“Mun samu labarin wani mahauci Ifeanyi Egwuagu ya rasa ransa sakamakon sara da ya sha a hannun abokinsa Michael Kingsley wanda suke zaune gida daya, amma Kingsley ya tsere bayan tafka danyen aikin. Da isar mu wajen da lamarin ya auku, sai muka garzaya da Ifeanyi zuwa asibiti, a can ne ya riga mu gidan gaskiya.” Inji Kaakakin.

Wani matashi ya rasa ransa a sanadiyyar shiga tsakanin wasu yan giya dake faɗa

Kurkuku

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito Yansanda sun samu nasarar cafke mutumin, inda ya amsa laifinsa, tare da tabbatar da abota dake tsakaninsa da mamacin, sai dai yace sun samu matsala ne bayan ya siyan ma wani abokinsa,Ogidi giya su sha, amma Ogidi ya bukaci ya karo musu, shi kuma ya ga ba zai iya ba, sai ya ki.

Kingsley yace wannna ne yasa suka fara cacan baki da abokin nasa, har ta kai ga sun fara fada, inda kowa ya fasa kwalba, ana cikin haka ne sai tsautsayi ya jefo mamacin, wanda yayi kokarin shiga tsakaninsu, a nan Kingsley ya daba ma mamacin kwalba har sau biyu, nan take ya fadi yana shure shure, shi kuma sai ya arce.

Daga karshe Kaakakin yace zasu cigaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel