Wani uba ya kashe jaririyar sa mai kwanaki 21 a duniya da mari

Wani uba ya kashe jaririyar sa mai kwanaki 21 a duniya da mari

Labarin da muke samu daga rundunar 'yan sandan jihar Legas na nuni ne da cewa wani uba mai suna Edet Asuquo ya tsere ya bar gidan sa bayan da ya shararawa diyar sa mari mai kwanaki 21 kacal a duniya.

Haka nan dai 'yan sandan sun bayyanawa majiyar mu cewa uban ya mari jaririyar ne dai saboda kawai tana jinsin mace domin a cewar sa bata da wani anfani.

Wani uba ya kashe jaririyar sa mai kwanaki 21 a duniya da mari

Wani uba ya kashe jaririyar sa mai kwanaki 21 a duniya da mari

KU KARANTA: Wani miji ya saki matar sa saboda yawan haihuwa

Legit.ng dai ta samu cewa shi dai uban ya mari jarijiyar ne bayan ya dawo gida ya tarar da ita tana ta kuka ba kakkautawa sakamakon yunwar da take ji inda ya bayyana bacin ran shi.

A wani labarin kuma, Wani kasurgumin barawo dake badda kama kamar ta mahaukaci mai suna Olayinka Ogundamiro ya shiga hannun jami'an tsaron rundunar 'yan sandan Najeriya na shiyyar jihar Legas bayan da dubin sa ta cika.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu, Mista Ogundamiro mai shekaru 25 kacal a duniya ya shiga hannun 'yan sandan ne a ranar Litinin din da ta wuce tare da wata jikkar sa da aka samu wayoyin hannu masu tarin yawa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel