Gwamnatin tarayya za ta saki fursunoni 368 a jihar Kano

Gwamnatin tarayya za ta saki fursunoni 368 a jihar Kano

A cikin shirin rage cunkoso a gidajen yari dake fadin kasar nan, gwamnatin tarayya ta kudiri aniyyar sakin fursunoni 368 a jihar Kano.

Ministan shari'a kuma lauyan kolu na kasa, Abubakar Malami, shine ya bayyana hakan a yayin da mambobin kwamitin masu ruwa da tsaki akan shirin rage cunkoson gidajen yari suka kai ziyarar aiki fadar gwamnatin jihar a ranar Talatar da gabata.

Malami ya jinjinawa gwamnan a sakamakon jagorantar yaki na fafutikar neman rage cunkoson gidajen yari, inda yace Kano ita ce jiha ta farko a kasar nan wajen shigewa gaba domin aiwatar da wannan kuduri.

Cunkoso a gidajen yari

Cunkoso a gidajen yari

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi afuwa ga fursunoni 500 a yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar, wanda a yanzu gwamnan zai sake yiwa fursononi 368 afuwa wajen biyan musu tara.

KARANTA KUMA: 'Yan takara 725 zasu fafata a zaben kananan hukumomin jihar Filato

A nasa jawabin, Ganduje ya bayyana farin cikinsa dangane da yadda jihar Kano ta kasance jihohin farko da kwamitin ya ziyarta domin tabbatar da rage cunkoson gidajen yari bisa ga bin umarnin shugaba Buhari.

Ya kara da cewa, kawowa yanzu gwamnatinsa ta yiwa fursunoni sama da 1500 afuwa da suka aikata kananan laifuka a sakamakon gazawarsu ta biyan tara.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel