Yan Najeriya sun shaida ina iyakan kokarina - Shugaba Buhari

Yan Najeriya sun shaida ina iyakan kokarina - Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Gambiya a yau

- Sun tattauna akan abubuwan da ya faru lokacin aka cire Yahya Jammeh daga mulki

A yau Talata, 16 ga watan junairu Shugaba Muhammadu Buhari yace yan Najeriya sun shaida kuma sun amince gwamnatinsa na iyakan kokarinta duk da babu sauki.

Game da cewar mai magana da yawunsa, Garba Shehu, shugaba Buhari ya yi jawabi ne yayind yake karban bakuncin shugaban kasan Gambiya, Adama Barrow a fadar shugaban kasa.

Shugaba Buhari ya ce gwamnatin da ya gada ta samu dukiyoyin da ba'a taba samu ba a tarihin kasar.

Yan Najeriya sun shaida ina iyakan kokarina - Shugaba Buhari

Yan Najeriya sun shaida ina iyakan kokarina - Shugaba Buhari

Yace: " Kashi 60 cikin 100 na mutane Miliyan 180 yan kasa da shekaru 25 ne. Dukkansu na neman rayuwa mai kyau. Wadanda sukayi karatu na ganin cewa sune sukafi cancanta da aiki."

KU KARANTA: Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin shugaban kasar Gambia, Adama Barrow

“Mun karanci matsalan kuma muna iyakan kokarinmu wajen magance matsalan.

Mun gaji wani gwamnati ne wacce ta rike ragamar mulki shekaru 16. A wadannan shekaru, kasar ta samu dukiyoyin da bata taba samu ba a tarihin kasar.

Amma mun san ko yaya ne, mutane na amincewa da muna iyakan kokarinmu."

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a

http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel