Da ɗumi ɗumi: Hukumar EFCC ta turke tsohon gwamnan jihar Filato a Abuja

Da ɗumi ɗumi: Hukumar EFCC ta turke tsohon gwamnan jihar Filato a Abuja

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagin kasa, EFCC, ta cika hannu da tsohon gwamnan jihar Filato, Jonah Jang a ranar Talata 16 ga watan Janairu.

Premium Times ta ruwaito tun da safiyar Talata ne jami’an hukumar suka fara yi ma Jonah Jang tambayoyi a babban ofishinsu na babban birnin tarayya Abuja kan wasu bahallatsar kudade da suke tuhumarshi da shi.

KU KARANTA: Kungiyoyin Musulmai sun gwabza a kan lokacin Sallar juma’a, mutum 1 ya mutu

Jonah Jang ya shugabanci jihar Filato ne daga shekarar 2007 zuwa 2015 a karkashin inuwar jam’iyyar PDP, kuma a yanzu shine Sanatan al’ummar mazabar Filato ta Arewa.

Da ɗumi ɗumi: Hukumar EFCC sun turke tsohon gwamnan jihar Filato a Abuja

Jonah Jang

Sai dai majiyar Legit.ng ta ruwaito hadimin tsohon gwamnan, Olivia Dyzam ya musanta wannan batu, inda yace Maigidan nasa ya amsa gayyatare hukumar EFCC ne, don haka ba kama shi suka yi ba.

Silar wannan gayyata na hukumar EFCC shi ne wani bincike da gwamnatin jihar Filato ta Simon Lalong ke yi game da badakalar kudade da gwamnatin Jonah Jang ta yi, wadanda suka tasar ma biliyoyin nairori.

Dama dai ko a satin data gabata sai da hukumar ta aika ma Sanatan takardar gayyata, amma yayi kunnen uwar shegu yaki amsa kiran hukumar, inda yace yana da muhimman aiki a gabnsa ne, har sai da suka ci caraf da shi a yau.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel