Hukumar EFCC ta gurfanar da dan tsohon gwamna saboda cuwa-cuwan N92m

Hukumar EFCC ta gurfanar da dan tsohon gwamna saboda cuwa-cuwan N92m

- EFCC ta tuhumi dan Sanata Abdullahi Adamu, mai suna Mohammed Adamu da cuwacuwan naira miliyan 92

- Sanata Abdullahi Adamu shi ne Sanata mai wakiltar Yammacin Nasarawa kuma shi ne tsohon Gwamnan Jihar

- Za a gurfanar da Adamu ne a ranar Laraba a wata Babbar Kotun Tarayya a Kano

A ranar Laraba ne Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), zata gurfanar da Mohammed Adamu a kotu bisa tuhumar cuwacuwa ta naira miliyan 92. Mohammed Adamu da ne ga tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, kuma Sanata mai wakiltar Yammacin Nasarawa a yanzun.

Mai magana da yawun Hukumar, Mista Samin Amaddin, ya bayyana cewan za a gurfanar da Adamu ne gaban wata Babbar Kotun Tarayya a Kano, tare da wani mai suna Felix Ojiako, bisa laifuka 5 da su ka danganci almundahanar kudi.

Badakalar kudi N49m: EFCC ta gurfanar da dan wani Sanata gaban kotu

Badakalar kudi N49m: EFCC ta gurfanar da dan wani Sanata gaban kotu

DUBA WANNAN: Zargin badakalar N450m: Baban Lauya ya ce babu tuhuma a kansa, ya bukaci kotu ta sallame shi

An fara binciken su ne sakamakon korafi da Daraktan Gudanarwa na Kamfanin Biolocks Technologies, mai suna Atta Esin, ya yi. Esin ya zarge su da yin amfani da sunan kamfanin na sa wurin yin cuwacuwar kwangila da kuma cogen haraji har na naira miliyan 1.3.

A bayanin da Esin ya gabatar, cuwacuwan kwangilan da su ka yi ya kai na naira miliyan 26. Sai dai kuma bincike ya nuna cuwacuwan ya kai har na naira miliyan 92.

Bayanai kuma sun nuna cewan a na zargin wadanda a ke tuhumar da yin takardun boge na kamfanin wanda ya ba su damar bude asusun banki wanda ta cikin sa ne su ka aiwatar da cuwacuwan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel