Wata kotun Najeriya ta yi watsi da karar wata mata bisa zarginta da fashi da makami

Wata kotun Najeriya ta yi watsi da karar wata mata bisa zarginta da fashi da makami

- Wata babbar kotu ta yi watsi da karar wata mata da ake zargi da aikata fashi

- Kotun ta ce ba'a shigar da karar bisa ka'ida ba

- Masu kara sun gaza gabatar da shaidunsu

Mai shari'a, Afamefuna Nwobodo, dake wata babbar kotu a jihar Enugu ya wanke wata mata, Onyeka Okpala, da ake zargi da aikata laifin fashi.

Alkalin kotun ya ce ya wanke wacce ake karar ne saboda rashin bin ka'idoji wajen gurfanar da ita a gaban kotun sannan ga kurakurai da aka tafka wajen shigar da karar.

Wata kotun Najeriya ta yi watsi da karar wata mata bisa zarginta da fashi da makami

Wata kotun Najeriya ta yi watsi da karar wata mata bisa zarginta da fashi da makami

Mai gabatar da kara, J. E. Enyeagha, ta fadawa kotu cewar karar da ake saka ran sauraron ta a yau ta samu cikas saboda rashi bayyanar shaidun masu kara a kotun, tana mai bayyana cewar duk kokarinta na hada kan shaidun ya ci tura.

DUBA WANNAN: 'Yan Najeriya 14 da aka yankewa hukuncin kisa a Madinah sun aiko wa da Buhari sako

Kazalika lauyar dake kare wacce ake kara, Ifeoma Okeke, ta ce wacce take karewa ba ita ce ta aikata laifin fashin ba. Sannan ta kara da cewar a takardar karar dake gaban kotu ana zargin wasu mutane biyu ne da laifin yi wa wani Osuji Alberto fashin wayar sa ta hannu da kudi N300,000.

"Wadanda ake zargi da aikata laifin maza ne guda biyu ba mace ba. Wacce nake karewa bata aikata kowanne laifi ba, shi yasa tun fara shari'ar nan a shekarar 2011 bata taba fashin zuwa kotu ba," a cewar lauya Okereke.

Okereke ta roki kotu da ta yi watsi da dukkan zarge-zarge dake kan wacce take karewa, Okpala.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel