Dalilin da ya sa muka dauki tsauraran matakai domin ganin Jammeh ya sauka - Buhari

Dalilin da ya sa muka dauki tsauraran matakai domin ganin Jammeh ya sauka - Buhari

- Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana dalilin da yasa shugabanin kasashen Afrika suka tursasa ma tsohon shugaba Yahya Jammeh sauka daga mulki

- Yayha Jammeh dai ya ki sauka daga mulkin ne duk da cewa sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 1 ga watan Disamba ya nuna cewa bai yi nasara ba

- Shugaba Muhammadu Buhari yace sunyi rarashi da kuma bashi shawarwari amma yaki ji, hakan yasa basu da wata abin da ya rage face daukan tsatsauran matakin

Shugaba Muhammadu Buhari ya nuna takaicin sa ga yadda shugabanin tsohon shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya ki sauka daga mulki ta laluma duk da cewa ya fadi zabe har sai da shugabanin kasashen Afirka suka tursasa shi.

Dalilin da yasa muka tursasa wa Jammeh ya sauka daga mulki - Buhari

Dalilin da yasa muka tursasa wa Jammeh ya sauka daga mulki - Buhari

KU KARANTA: Zargin badakalar N450m: Baban Lauya ya ce babu tuhuma a kansa, ya bukaci kotu ta sallame shi

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin da ya karbi bakuncin shugaban kasar Gambia, Mista Adama Barrow a Fadar Aso Villa da ke Abuja, Buhari ya ce Najeriya da sauran kasashen ECOWAS ba su da yadda za su yi illa tilasta masa saukan.

Shugaba Buhari kuma ya tunatar da shugabanin kasashen Afrika da cewa sai sun karfafa hukumomin demokradiya kafin nahiyar za ta cigaba sosai kamar sauran nahiyoyin duniya.

Ya yi kira ga Shugaban kasar Gambian da ya cigaba da gudanar da ingantacen zabe wanda al'umma za suyi na'am dashi domin hakan ne babban abin da zai sa a samu demokradiya mai dorewa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel